Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai Ja-goran juyin musulunci, Ayatullahi sidi Aliyu Khamaina'i ,a wani jawabi da ya yi a yayin da yake ganawa da dangin shahidai, da wadanda suka ji rauni a kallafaffen yaki da suka yi da kasar Iraki, ya karfafa muhimmancin fada da ta'addanci a duk fadin duniya, kuma ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai biranen New York da washington na kasar Amirka, sannan ya bayyana cewa akwai kura-kurai da nuna girman kai kwarai da yadda kasar Amirka take kallon ayyukan ta'addanci, irin wanda duk mai hankali ba zai taba yarda ba . Ja-goran ya bayyana cewa, kasar jumhuriyan musulunci ta Iran bata ganin kasa irin Amirka ta cancanci ta ja-goranci harkar fada, ko yaki da ta'addanci a duniya, don kuwa kasar Amirka tana da hannu dumu-dumu a ayyukan ta'addanci da dama, da aka aikata a duniya. Kuma kasar jumhuriyan musulunci ta Iran bata ganin kasar Amirka da gaske take yi wajen fadan da ta daura da ta'addanci, tana da wata manufa a boye. Ja-goran ya kara da cewa abin da ya faru a biranen New York da Washington ya sanya kasar da kuma shuwagabannin Amirka cikin rudu da girman kai wanda bai kamata a nunawa kasashe masu 'yanci a duniya ba. A yayin da yake magana a kan maganar da ke cewa duk wanda ba ya tare da kasar Amirka to yana tare da 'yan ta'adda, ja-goran ya ce "wannan zancen banza ne kawai, don a halin yanzun kasashen da suke tare da kasar Amirka sun fi kowace kasa ta'addanci a duniya. A halin yanzu in ja-jagoran wadanda suke ja-gorancin haramtacciyar kasar Isra'ila suna da hannu a ayyukan ta'addanci, mafi muni da tsoratarwa a duniya, kuma a halin yanzu da nake magana suna ci gaba da ayyukansu, don haka wannan magana ba karbabbiya ba ce a wajenmu, mu ba ma tare da kasar Amirka kuma ba mu tare da 'yan ta'adda. Ja-goran ya kara da cewa "a ganin Amirka, kashe-kashe "Sabra, kana, da Shatila , da kuma kisan musulman Falasdinu da Yahudawan Isra'ila suke yi a kullum ba ayyukan ta'addanci ba ne, amma kare kai, da kuma gwagwarmayar musulmin Falasdinu kan kasar su da aka kwace shi ne ta'addanci . Ja-goran juyin musulunci ya kara da cewa "shuwagabannin kasar Amirka suna raba 'yan ta'adda kashi biyu, masu kyau da marasa kyau, amma mu a wajenmu duk ba su da kyau. Harbe jirgin saman fasinja na kasar Iran da kasar Amirka ta yi a kan sararin samaniyan Tekun Farisa, inda ta kashe mutanen da ba su da laifi, ba ma kawai kasar Amirka bata nemi gafaran kasar Iran ba ne kawai, ko ta tausayawa wadanda ta kashe ba, a'a kasar Amirka ta ba da lada ga kwamandan sojojin ta da suka yi wannan aika aikan.
Ayatullahi Khamina'i ya yi suka ga kafafen watsa labaru kan yadda suka koma bangare guda, tun lokacin da hatsarin biranen New York da Washington suka auku, sun koma wajen watsa manufofin kasashe masu fada a ji kawai, kuma sun koma wajen farfaganda kan batanci ga addinin musulmi. Ja-goran ya ce "me ya sa da zarar hatsarin New York da Washington na aukuwa kuka yi gaggawa wajen tuhumar musulmai, a yayin da kuke raya cewa shirye-shiryen tsaronku ya fi na kowacce karfi, me ya sa jami'an tsaron ku suka kasa gano wannan dasisan wanda ke bukatan watanni ko ma shekaru kafin a aiwatar da su? A yayin da yake bayani kan zancen shugaban kasar Amirka cewa "yakin salib ne za su yi" wato yakin yada kiristanci, ja-goran ya ce "Idan ba da wata manufa ba ne, me yasa irin wadannan maganganu masu hatsari suke fitowa daga bakin shugaban wata kasa wanda ba ya taka tsan-tsan wajen maganganun da suke fitowa daga bakin sa? Ayatullahi Khamina'i ya ce "ku kuka watsa maganganu wadanda suke suka ga musulmi da musulunci, kuma kuka watsa sunayen musulmi da larabawa wadanda kuke tuhuma, ba tare da kun ambaci ko da daya daga cikin Amirkawa ko 'yan yammacin Turai da kuke tuhuma ba, amma kuma kuke cewa musulmi, ai musulunci zaman lafiya ne ,kuma kaza da kaza ne" Ja-goran ya kara da cewa "neman taimako daga kasashen duniya da kasar Amirka take yi don an taba amfaninta ne, kuma ba gaskiya take nufi cikin al'amarin ba. Don irin wannan halin nata ne ya sa, a yau muna gani a kasashe da dama mutane suna ta kona tutar kasar Amirka. Kuma taron yaki da babancin launin fata da a ka yi a kasar Afrika ta Kudu, ya bayyana a fili irin yadda mutanen duniya suke adawa da manufin kasar Amirka . Ja-goran ya ce, kamar yadda jami'an gwamnatin jumhuriyar musulunci ta Iran suka sha bayyanawa a ganeganen su da tattaunawa, ba laifi ni ma na sake fada don amfanin jama'a, cewa, jumhuriyar musulunci ta Iran ba za ta hada kai da kasar Amirka a shirin kai hari da ta ke son yi a kasan Afganistan ba, kuma ba za ta taba shiga cikin duk wata harka a duniya wanda kasar Amirka take ja-goranci ba . Makirce-makircen kasar Amirka kan kasar Iran a cikin shekaru 23 da suka gabata, a fili suke, kasar Amirka ta gurgunta amfanin kasar Iran da dama, da wane dalili kuma, in ji ja-goran take neman taimakon kasar Iran don an taba amfaninta? Ko tana tsammanin za mu taimaka wajen kai hari ga kasan Afganistan wacce take fama da wahaloli, kuma makobtanmu ne ? Ayatullahi khamina'i ya ce 'munufar kasar Amirka wajen kai wa kasan Afganistan hari, don wasu da suke tuhuma ,wanda har yanzun bai tabbata ba, wai suna boye a can, bai fi don ta kafa sansanonin sojojin ta a yankin Tekun Farisa da yankin Asiya ta tsakiya, da kuma kan iyakokinmu na gabas. Ja-goran ya ce, kasar Amirka bata cancanci ja-gorantar harkan fada da ta'addanci ba, kuma majalisan dinkin duniya tana iya ja-gorantan fada da ta'addanci ne kawai, da sharadin rashin tsoma hannun kasar Amirka da manya-manyan kasashen duniya don cimma manufofin su. Kuma nauyi mai yawan gaske, in ji ja-goran, na fada da ta'addanci ya hau kan kungiyan kasashen musulmi, wanda ya zama dole kungiyar ta shiga fage a matsayin kungiya mai 'yanci . Har ila yau ja-garan ya bayyana cewa nauyin kungiyar kasashen musulmi ne su yi wani abu kan mutanen kasan Afganistan wadanda suka yi ta fama da wahalhalu don shigan wasu kasashe cikin al'amarin makoman kasar, ya ce mutanen kasar Afganistan mutane ne jarumai, wadanda suke da kyawawan al'adu, ba abin da ya bambanta su da mutanen sauran kasashen duniya, jinin mutanen da suka mutu a hare-haren Washington da New York bai fi na mutanen Afganistan da a ke son zubar da jinin su ba . A wani bangare na jawabinsa, ja-goran ya bayyana cewa shahada a tafarkin Allah ta'ala shi ne abu mafi daraja da musulmi zai samu, ya ce "wadanda suka shiga kallafaffen yakin kare iyakokin kasarmu, musamman shahidai suna da wani hakki a kan duk mutanen kasar Iran. Kuma wadannan da suke zargin sojojinmu da 'yan (basiji ), basa kula da maslaha da kuma bukatun kasa. Kuma dole ne mutane su gane cewa ,makiya suna kokarin yin watsi da irin gwagwarmayan shekaru takwas da mutanen kasar Iran suka yi kan kare kasar su, amma dole ne mu fahinci cewa, dangogin shahidanmu abin alfahari ne garemu, kuma dole ne mu girmama su . A karshe Ja-goran ya bayyana watannin Rajab da Sha'aban a matsayin watanni ne na shirin shiga wata mai alfarma ta Ramadana . HOME |